Iran ta ƙirƙiri wani shu'umin jirgin yaƙi mai layar zana
Iran ta ƙirƙiri wani sabon jirgi mara matuki da ta yi masa laƙabi da Hadid 110, wanda ke da
Wani matsanancin gudu cikin ƙanƙanin lokaci kuma ƙasa-ƙasa, sannan yana iya kai farmaki cikin wani yanayi mai kama da layar zana domin kuwa ba a ganinsa har sai bayan ya ƙaddamar da hari.
Wallafawa ranar:
Jaridar The Telegragh ta Birtaniya ta rawaito cewa, yana da matuƙar wahala wani ya hangi gilmawar wannan jirgin mara matuƙi domin kuwa yana gudun sama da mil 300 cikin sa'a guda.
An bayyana sabon jirgin mara matuƙi a matsayin mafi tsananin gudu da Iran ta mallaka a tarihinta, yayin da ake ganin tsananin gudunsa, wata babbar dama ce ga Iran a fagen-daga.
Jaridar ta ce, Iran ta ƙirƙiri wannan sabon jirgin ne mara matuƙi domin ya rika ratsa garkuwar tsaron sararin samaniyar Amurka
Rundunar Juyin-Juya-Hali ta Iran ta bayyana cewa, a karon farko ta cilla wannan jirgin kan sansanonin sojin Amurka da kuma jiragen ruwan yaƙinta da ke jibge a yankin Gabas ta Tsakiya makwanni biyu da suka shuɗe.
Jaridar Telegraph ta gano cewa, Iran ta inganta sabon jirgin ne domin maye gurbin tsohon jirginta mara matuƙi na Hadid wanda take ɗauka a matsayin ɗaya daga cikin miyagun makamanta na yaƙi.
Babban banbancin da ke tsakanin sabo da tsohon nau'in jirgin mara matuƙi shi ne, matsanancin gudu da kuma layar zana.
Sabon jirgin na Hadid 110, an ƙirƙire shi domin kaddamar da farmaki gabanin na'urar tsaron sararin samaniya ya hango tare da kakkaɓo shi kamar dai yadda masana na Iran suka bayyana
Tun a bara, aka fara kaddamar da jirgin a gaban marigayi tsohon Jagoran Addinin Musulunci a Iran, Ali Khamenei gabanin a kashe shi a hare-hare haɗin guiwar Amurka da Isra'ila kamar yadda Telegrah ta rawaito.



Comments