Da gaske Mommy gwambe fasikace rigima tadau zafi

 DA GASKE MOMMY GOMBE FASIKA CE KO A'a: A Musulunci, fasikanci yana nufin fito na Fito ko kin biyayya ga Allah akan hanyar aikata manyan zunubai ko ci gaba da aikata laifuffuka ba tare da tuba ko barin Aikata Wannan abun ba.


Kalmar ta samo asali ne daga Larabci "fisq" (فسق), wacce ke nufin fita daga hanya madaidaiciya ko sabawa umarnin Allah.


Misalai na fasikanci sun haɗa da:


Yin zina.


Shan giya ko sauran abubuwan maye.


Yin sata.


Yin ƙarya da yaudara.


Cin hanci.


Zaluntar mutane.


Barin wasu manyan wajibai na Bautawa Allah ko Biyayya garesa da gangan ba tare da uzuri ko Hujja ba.


A cikin Al-Qur'an, Allah Ya ambaci fasikai a wurare da dama, misali:


"Lalle Allah ba Ya shiryar da mutane fasikai." (Suratul Munafiqun 63:6)


Saboda haka, fasiki shi ne mutumin da yake aikata sabo a fili ko, ya nace kan manyan zunubai ba tare da tuba ba. Amma idan mutum ya tuba da gaske, ya Daina Allah Mai yawan gafara ne kuma Mai jin ƙai.


Wannan shine Cikkakiyar Ma'ana Kalamr Fasik ba iya Mazinaci bane Fasiki zaka iya zama ko ki zama Fasiki ko Fasika ba tare da kataba yin Zina ba ko kin taba yin Zina Allah yasa mudace ya Tsaremu Amen.

Comments

Popular Posts