Skip to main content

Featured

Innalillahi wa inna ilaihi raji'uñ rasuwar zee diamond 💎 ta gargiza kanny wood

 Jiya tana cikin waɗanda mutane ke addu’ar Allah Ya ba su lafiya.  Yau kuma, abin da ya rage wa iyalanta, abokan aikinta da masoyanta shi ne addu’ar Allah Ya gafarta mata.  Wannan shi ne labarin da ya karya zuciyar masu kallon shirin Labarina a safiyar yau Litinin. An samu labarin rasuwar jarumar Zee Diamond, wadda aka fi sani da rawar Talatuwa Babar Bintalo, bayan ta shafe watanni tana fama da rashin lafiya. Rahotanni sun ce jarumar ta rasu ne da asubahin yau Litinin. Zee Diamond ta kasance daga cikin jaruman da masu kallon Labarina suka saba gani kuma suka sani ta hanyar rawar da take takawa, musamman matsayin Talatuwa Babar Bintalo. Rasuwarta ta zama babban rashi ga iyalanta, abokanta, abokan aikinta da kuma masoyan da suka saba ganin ta a cikin shirin. Wannan rasuwa ta sake tunatar da mutane yadda yanayin rayuwa kan sauya cikin lokaci.  Wanda mutane ke yi wa addu’ar samun lafiya a wani lokaci, cikin ƙanƙanin lokaci sai a koma yi masa addu’ar samun rahama. A wanna...

Yaki ya dawo sabo

 Izra@ila takai farmaki a cikin kasar Iran a matsayin ramuwa inda aka jiyo karar fashewa mai karfi a Tehran da Isfahan tare da wasu yankuna na kudancin Iran...


A yanzu haka Iran ta cigaba da kai hare hare masu nauyi zuwa cikin kasar Izra@ila ba tare da kakkautawa ba, tun daga arewacin kasar zuwa kudanci da birnin Tel Aviv...



Dakarun kasar Yemen suma sun shiga yakin inda suka takai hare hare zuwa kudancin Izr@ael da wasu sassan kasar...


Haka nan an hango makamai a sararin samaniya wadanda dakarun Labanon suka harba zuwa Arewacin Izra@ila..


Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa ba da sa hannunta bane Izra@ila ta mayar da martani ga Iran, amma sai dai hakan bai hana dakarun Iran kai hari akan sansanin sojan Amurka dake kasar Saudiyya ba.....


A takaice dai yaki ya dawo, addu'ar mu Allah ya bawa Iran da sauran musulmai nasara...

Comments

Popular Posts