Ummmi Lollipop
Fadila Muhammad, wadda aka fi sani da Ummi Lollipop, ta kasance daya daga cikin fitattun jaruman masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood.
An haife ta a shekarar 1993 a unguwar Unguwan Rimi, Jihar Kaduna, Najeriya. Mahaifinta dan asalin Jihar Borno ne, yayin da mahaifiyarta Bafulatana ce daga Yola, Jihar Adamawa.
Tun tana karama aka san ta da halin kirki, fara’a da mutunta mutane, abubuwan da suka sa take samun karbuwa a duk inda ta shiga.
A bangaren ilimi, Ummi Lollipop ta yi karatunta na lafiya a Makarfi School of Health Technology da ke Jihar Kaduna, inda ta samu horo a fannin kiwon lafiya.
Duk da cewa ta yi karatu a wannan fanni, sha’awarta ga harkar nishadi da fina-finai ta sa ta shiga masana’antar Kannywood a tsakanin shekarun 2017 zuwa 2018.
Ta fara samun suna ne bayan fitowarta a cikin fim din “Hubbi”, inda ta yi aiki tare da manyan taurarin Kannywood kamar Ali Nuhu da Adam A. Zango.
Kwarewarta wajen fitowa a fina-finai da kuma kyakkyawar mu’amalarta da jama’a sun sa ta samu karbuwa cikin sauri a masana’antar.
Saboda halinta na kirki, tausayi da fara’a, abokai da masoyanta suka lakaba mata sunan “Lollipop”, wanda ya zama sunan da aka fi santa da shi.
A rayuwarta ta sana’a, Ummi Lollipop ta kasance mai mutunta mutane kuma mai nisantar cece-kuce.
Ta gina suna mai kyau a masana’antar Kannywood, inda furodusoshi, daraktoci da abokan aikinta suka dinga yabawa da ladabi, biyayya da kwazo da take nunawa a wurin aiki.
Sai dai kaddara ta riske ta ne bayan ta sha fama da matsalar ciwon zuciya. A ranar 28 ga Agusta, 2020, tana da shekaru 27 kacal, ta rasu a cikin motar mahaifinta yayin da ake kokarin kai ta asibiti a garin Kaduna domin samun kulawar likitoci.
Rasuwarta ta girgiza masana’antar Kannywood da ma masoyanta a fadin Najeriya.
Bayan mutuwarta, manyan jarumai, furodusoshi da masu shirya fina-finai sun yi ta aika sakonnin ta’aziyya da jimami, suna bayyana irin gudummawar da ta bayar ga masana’antar da kuma kyawawan halayenta.
Mutane da dama suna tuna ta a matsayin jaruma mai hazaka, mai mutunci da kuma mace mai son zaman lafiya.
Duk da gajeruwar rayuwarta, Fadila Muhammad (Ummi Lollipop) ta bar tarihi mai kyau a Kannywood, kuma har yanzu ana ci gaba da tuna ta saboda kyawawan ayyukanta da dabi’unta nagari.
#labaranyau



Comments