Skip to main content

Featured

Innalillahi wa inna ilaihi raji'uñ rasuwar zee diamond 💎 ta gargiza kanny wood

 Jiya tana cikin waɗanda mutane ke addu’ar Allah Ya ba su lafiya.  Yau kuma, abin da ya rage wa iyalanta, abokan aikinta da masoyanta shi ne addu’ar Allah Ya gafarta mata.  Wannan shi ne labarin da ya karya zuciyar masu kallon shirin Labarina a safiyar yau Litinin. An samu labarin rasuwar jarumar Zee Diamond, wadda aka fi sani da rawar Talatuwa Babar Bintalo, bayan ta shafe watanni tana fama da rashin lafiya. Rahotanni sun ce jarumar ta rasu ne da asubahin yau Litinin. Zee Diamond ta kasance daga cikin jaruman da masu kallon Labarina suka saba gani kuma suka sani ta hanyar rawar da take takawa, musamman matsayin Talatuwa Babar Bintalo. Rasuwarta ta zama babban rashi ga iyalanta, abokanta, abokan aikinta da kuma masoyan da suka saba ganin ta a cikin shirin. Wannan rasuwa ta sake tunatar da mutane yadda yanayin rayuwa kan sauya cikin lokaci.  Wanda mutane ke yi wa addu’ar samun lafiya a wani lokaci, cikin ƙanƙanin lokaci sai a koma yi masa addu’ar samun rahama. A wanna...

Tarihin Abba Al mustapha

 Abba El-Mustapha (an haife shi a 21 ga Janairu, 1978) cikakken sunansa shine Abba Mustapha Inuwa, fitaccen jarumi ne, furodusa, darakta kuma ɗan kasuwa a masana’antar Kannywood. 


An haife shi a unguwar Dandago da ke ƙaramar hukumar Gwale a Jihar Kano, inda ya yi karatun firamare a Buk Staff Primary School (1984–1989) sannan ya halarci Kano State Foundation School (1989–1992) kafin ya kammala sakandare a Alhassan Usman College a 1995. 


Daga bisani ya samu digiri a fannin Kimiyyar Siyasa da kuma Ilimin Laburare tare da Digirin Digirgir (Master’s Degree) a Public Administration daga Bayero University Kano. 



Ya shiga harkar fim a 2002, kuma cikin sauri ya zama ɗaya daga cikin fitattun jaruman Kannywood, inda ya fito a fina-finai da dama kamar Ruda, Kamshi, Dausayi, Hakki, Jarumai, Girma, Feshi, Sakace da sauran su. 


A tsawon aikinsa ya samu lambobin yabo da dama ciki har da City People Movie Award da Kannywood Awards, yayin da ake girmama gudummawar da ya bayar ga masana’antar fina-finan Hausa. 


A bangaren rayuwa ta sirri, Abba El-Mustapha yana aure da Fatima M. Shuwa kuma suna da ’ya’ya uku. 


Dangane da sabbin abubuwan da suka shafe shi, a Fabrairu 2025 an karrama shi da Kannywood Legendary Award, yayin da wasu manyan masana harkar fina-finai suka yaba da gudummawar da ya bayar ga ci gaban Kannywood tare da ba da shawarar a ƙara girmama nasarorinsa a fannin fasahar fim. 


Har zuwa 2026, yana ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan jaruman Kannywood masu tasiri, tare da shiga harkokin cigaban masana’antar da kuma ayyukan al’umma.


#labaranyau

Comments

Popular Posts