Skip to main content

Featured

Innalillahi wa inna ilaihi raji'uñ rasuwar zee diamond 💎 ta gargiza kanny wood

 Jiya tana cikin waɗanda mutane ke addu’ar Allah Ya ba su lafiya.  Yau kuma, abin da ya rage wa iyalanta, abokan aikinta da masoyanta shi ne addu’ar Allah Ya gafarta mata.  Wannan shi ne labarin da ya karya zuciyar masu kallon shirin Labarina a safiyar yau Litinin. An samu labarin rasuwar jarumar Zee Diamond, wadda aka fi sani da rawar Talatuwa Babar Bintalo, bayan ta shafe watanni tana fama da rashin lafiya. Rahotanni sun ce jarumar ta rasu ne da asubahin yau Litinin. Zee Diamond ta kasance daga cikin jaruman da masu kallon Labarina suka saba gani kuma suka sani ta hanyar rawar da take takawa, musamman matsayin Talatuwa Babar Bintalo. Rasuwarta ta zama babban rashi ga iyalanta, abokanta, abokan aikinta da kuma masoyan da suka saba ganin ta a cikin shirin. Wannan rasuwa ta sake tunatar da mutane yadda yanayin rayuwa kan sauya cikin lokaci.  Wanda mutane ke yi wa addu’ar samun lafiya a wani lokaci, cikin ƙanƙanin lokaci sai a koma yi masa addu’ar samun rahama. A wanna...

Nafisa Mai capacity

 NAFISA ABDULLAHI fitattun jaruman mata da suka yi tasiri a Kannywood cikin shekaru da dama, Ta fara jan hankali ne tun bayan fitowarta a fim din Sai Wata Rana, fim dinda ya bude mata kofar shahara a fadin Duniya.


Daga wannan lokaci, Nafisa taci gaba da fitowa a fina-finai da dama tare da gina suna a matsayin daya daga cikin jaruman da suka fi samun karbuwa a Kannywood. Wakoki, fina-finai, tallace-tallace da harkokin kasuwanci duk sun taimaka wajen kara mata farin jini.



Abin da ya bambanta Nafisa da wasu shi ne yadda ta iya ci gaba da kasancewa cikin sahun gaba duk da sauye-sauyen da masana'antar ta fuskanta tsawon shekaru. Wasu na yabawa kwarewarta wajen acting, yayin da wasu ke ganin kwarin gwiwarta da yadda take tafiyar da rayuwarta ne suka kara mata masoya.


A yau, mutane suna kallon Nafisa Abdullahi a matsayin daya daga cikin jaruman da suka taimaka wajen daukaka martabar Kannywood a cikin Najeriya da ma kasashen waje.


#labaranyau #kannywood #kannywoodmedia #HAUSAMOVIE

Comments

Popular Posts