Cikken Tarihin Jamila labarina
Amina Uba Hassan, wadda aka fi sani da Jamila Labarina, Maman Haidar, ko Amina Rani, fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood ce, ‘yar fim, kuma mai shirya fina-finai, wadda aka haifa a ranar 25 ga Fabrairu, 1990, a Kaduna State.
Ta yi karatun firamare da sakandare a Kaduna, sannan ta samu difloma a fannin Mechanical Engineering daga Kaduna Polytechnic.
Amina ta fara harkar fim tun farkon shekarun 2000, kuma ta shahara sosai bayan fitowarta a matsayin “Jamila” a shahararren shirin Hausa na talabijin Labarina.
Ta auri fitaccen jarumin Kannywood Adam A. Zango a shekarar 2007, kuma suka haifi ɗa guda mai suna Aliyu Haidar a shekarar 2008, kafin daga bisani a raba aurensu bayan watanni kaɗan, wanda hakan ya sa aka fi saninta da suna “Maman Haidar.”
Bayan ta ɗan janye daga harkar fim na wasu shekaru, ta sake dawowa Kannywood a shekarar 2021, inda ta fito a fina-finai da shirye-shirye kamar Gidan Danja, Jarumi, Matar Alhaji, da Garwashi.
A shekarar 2026, Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano ta sanar da dakatar da Amina Uba Hassan tare da Adam Garba (Raba-Gardama) daga gudanar da harkar fim a jihar Kano na tsawon shekara guda, bisa dalilin fitowarsu a wani faifan bidiyo da hukumar ta bayyana a matsayin abin da ya saba da tarbiyya.
Sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Abubakar Sani, ya fitar ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da kiyaye ƙa’idojin ɗabi’a da hukumar ke jagoranta a masana’antar Kannywood.
Duk da wannan rikici, Amina Uba Hassan na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin fitattun jarumai a Kannywood, wadda aka san ta da ƙwarewa a wasan kwaikwayo da kuma gudunmawarta ga fina-finan Hausa.
#labaranyau



Comments