Skip to main content

Featured

Innalillahi wa inna ilaihi raji'uñ rasuwar zee diamond 💎 ta gargiza kanny wood

 Jiya tana cikin waɗanda mutane ke addu’ar Allah Ya ba su lafiya.  Yau kuma, abin da ya rage wa iyalanta, abokan aikinta da masoyanta shi ne addu’ar Allah Ya gafarta mata.  Wannan shi ne labarin da ya karya zuciyar masu kallon shirin Labarina a safiyar yau Litinin. An samu labarin rasuwar jarumar Zee Diamond, wadda aka fi sani da rawar Talatuwa Babar Bintalo, bayan ta shafe watanni tana fama da rashin lafiya. Rahotanni sun ce jarumar ta rasu ne da asubahin yau Litinin. Zee Diamond ta kasance daga cikin jaruman da masu kallon Labarina suka saba gani kuma suka sani ta hanyar rawar da take takawa, musamman matsayin Talatuwa Babar Bintalo. Rasuwarta ta zama babban rashi ga iyalanta, abokanta, abokan aikinta da kuma masoyan da suka saba ganin ta a cikin shirin. Wannan rasuwa ta sake tunatar da mutane yadda yanayin rayuwa kan sauya cikin lokaci.  Wanda mutane ke yi wa addu’ar samun lafiya a wani lokaci, cikin ƙanƙanin lokaci sai a koma yi masa addu’ar samun rahama. A wanna...

Adam a zango duniya ne

 Bikin Sallah a Kano ya kara daukar zafi yayin da shugaban mawakan Kaduna Adam A Zango, tare da tawagarsa suka halarci gagarumin taron nishaɗi da kungiyar Triple R Kannywood ta shirya a Gidan Zoo na tsawon kwanaki uku.



Taron ya hada dubban masoya nishaɗi yayin da mawaka, jarumai da masoya suka taru domin bikin Sallah cikin annashuwa da farin ciki.


Kasancewar Adam A Zango a wajen taron ya kara wa shagalin armashi, inda mutane da dama suka nuna jin dadinsu da yadda aka gudanar da taron 💯


Allah Ya kara masa lafiya, daukaka da cigaba, tare da dorewar farin ciki da hadin kai a tsakanin al’umma


#shateemahvibes #Sallah #AdamZango #TripleRKannywood #Kano #kannywood #kannywoodmedia

Comments

Popular Posts