Ina ma'abota hausa novels
MATAR TAJ(Destined with youπ©΅π€)
❤️π₯Romantic love story❤️π₯
Written by QueenMarh
Da sunan Allah mai rahama mai Jinkai…
Gargadi!! Ban yarda wani ya chanza min koda kalma daya bane daga cikin littafin nan batare da amincewa ta ba, sannan littafin nan na kudi ne,idan kinaso ki biya Saina tura maki And lastly bazanyi free page da yawa ba.
I hope you’ll enjoy this master piece guys, zaku tsinci tsaftattaciyar tsantsar soyayya aciki wannan littafi hade da cin amana da qiyyaya.
The suspense and the plot twist is a top notchππ
Enjoy!!!!!
Free page
Chapter 5-6
3 months ago (wata uku da suka wuce)
FCT Nigeria……….
Dutsen habuja wani gari ne dake a baya bayan garin abuja, yawancin mazauna garin basuda arzikin zama cikin ainihin garin Abuja,sai ya kasance masu zama a cikin garin zaman rufin asiri sukeyi saboda rayuwar Abuja sai mai arziki.
Acikin garin akwai anguwar datafi fuce a cikin garin wadda ake kira da kayefi, anguwace me qunshe da tarin jama’a don anguwar a cunkeshe take da mutane, both chiristians da musulmai harma da waenda basuda addini,a bangaren culture kuwa babu wanda babu a aguwar, gwari, yarbawa, igbo, igala duka,haka zalika ginin aguwannin cikin layin kwata kwata basuda kan gado don yawanci gidaje ne na haya barkate don ko hanyar da mota zata kutsa cikin layin babu.
Yawan mutanen anguwan yasa aka samu qarancin tsafta a anguwar saboda yanda mutane ke sana’a daban daban acikin anguwar don su rufa ma kansu asiri su samu na cin yau da gobe.
Da sallama wata dattijuwar mata ta shigo daya daga cikin gidajen haya a anguwar kayefi anan bayan garin Abujan,dan karamin gida ne daga waje mai kofar karfe, labulen zauren gidan ta dage inda ta sanya kafarta cikin tsakar gidan, hayaniyar da akeyi daga ciki ne ta karade tsakar gidan inda wasu mata da mazan gidan ke hada hadan su kowanne yana abunda ya shafe sa.
Wato daga cikin gidan dakuna ne kusan guda biyar a jere, sai dan tsukeken tsakargidan da bandaki sai wata yar rumfa da alamu anan sukeyin girki.
Ragowar Goron dake hannunta ta wulla cikin bakin ta kafin ta rike sandar dake taimakonta wajen tafiya don tana da kiba sosai gashi girma yazo don kamarma dan dingisawa takeyi, sanye dattijuwar take da atamfa riga da zani sai wani mayafi kore kore.
Tana karasowa tsakar gidan ta soma tari saboda hayaqin daya bade tsakargida inda yake fitowa daga rumfar girkin su.
Matan dake zaune a tsakar gidan sunsha daurin kirji sai faman zazzaga masifa suke tsakanin,daman sun saba, don dawuya ayi wuni guda ba tare da anyi fadan nan ba kamar kaji.
Mazajensu kuwa suna kallonsu ko qala bazasu ce masu ba, mazauna gidan maqotansu kuwa babu wanda yake shiga irin wannan fadan saboda daga hakan yake jawo babbar matsala.
Takalman kafafunta ta soma zarewa ta ture su gefe guda hannunta rike da leda, ta soma takowa daidai hanyar rumfar girki kafin ta dan leka tare da daga murya tace ‘’keeee sabeeha?? wannan hayakin fah? Babbake gidan zakiyi ne?’’
Yarinyar dake tsugunne a bakin wata runfa daga chan tsakar gida sai faman rura wuta take kamar ranta zai fita don iccen kwata kwata bashida cii saboda yanayin garin yau ayi rana gobe ayi ruwa, takai kusan awa guda a tsugunne tana faman abu daya, gashi rana ta fito kwal sosai don rufin langa langa ne wanda hakan yasa zafin ya hadar mata biyu ga zafin rana gana wuta don kusan kowa ya daura tukunyar girkin rana.
Jin sautin muryar kakarta yasa ta saurin juyowa ta mike tsaye don nufin hanyar fucewa daga rumfar,gyaran mataccen hijab din jikinta ta soma yi don yayi mata yawa sosai gashi ya kode,ta wajen wuyan hijab din ta tattaro shi ya rufe rabin fuskarta, babu abunda ake iya hangowa sai hazel eyes dinta da sukayi jaa masu daukar hankali da ido, gashin idanunta sunyi wara wara saboda hawayen dake zubo mata saboda hayakin data shaqa, wajen brows dinta kuwa a cike yake da gashi har yana neman hadewa baqi wuluk dashi.
Saida ta fito sarari sosai na kalleta dakyau, daga ganinta tana da dan haske saidai wahala data kodar da ita, bata da wani tsayi sosai saidai baza ace da ita gajeruwa ba, kana ganinta kaga yarinya danya shataf don bazata wuce shekaru sha bakwai zuwa sha takwas ba, hijab din jikinta yasa na kasa gane yanayin jikinta saidai bata da wani qiba, kafarta sanye da baqin silifas daya soma cinyewa.
Tari ta soma yi tana mutsiqa idanunta da sukayi jaa kafin cikin ladabi ta soma Magana tana mai kokarin karbar ledar hannun inna ‘’sannu da dawowa inna’’
Kallon fuskanta inna tayi idanunta yayi jaa sosai gashi sai kaurin hayaki takeyi ga uban zufa data tsatsafo mata.
Adan fada fada inna ta soma Magana ‘’wannan hayaqin fa? Ni mai larurar idanu ay sai ki karashe min ganin nawa ‘’
Inna ta karashe tana mata wani irin kallo, shuru yarinyar data kira da sabeeha tayi tana mai sauraronta saida takai aya tukunna kafin ta soma Magana cikin ladabi.
‘’inna iccen ne ba…ya ci’’.
‘’ke har yanxu hada icce ya zame maki wani jan aiki,ina uwar taki’’
Kanta ta sauke kasa tana mai duban jar kasan dake tsakar gidan don ko sumunti ba ayi ba ,’’bata dawo ba ’’ ta bata amsa
Saurin runtse idanu inna tayi don yana yanar da idanun nata keyi cikin yan kwanakin nan yasa ganin ta ke neman daukewa dukda bata bari kowa yasan da yanayin da take ciki ba.
‘kin gama dahuwar kwan?’’ ta sake wullo mata tambaya
‘’eh na gama tun daxu, abunci rana ne nake kokarin daurawa’’ ta bata amsa a natse.
‘’zoki bani ruwa mai sanyi in kashe kishirwar dana kwaso,’’
Tana kaiwa nan ta nufi hanyar dazai sadata da dakin su, kofar dakinsu na daga chan saqo, daga gefe kuma wani daki ne karami.
‘’inna ka dawo’’ wata matar gwari dake kokarin daurama yarta robar dafaffiyar masara ta sayarwa ta soma Magana.
Kallon inda take inna tayi kafin ta washe baki don ita kadaice suke mutunci a gidan dan sauran kwata kwata basuda mutunci ‘’maman chidi na dawo, ina chidin yake’’
‘’shege yaro ya tafi yawo’’ matar ta bata amsa
‘’yara daman ba’a rabasu da yawo, miqon masarar hamsin’’ ta karashe tana wucewa
‘’toh,’’
Karbar masarar sabeeha tayi kafin ta bi bayan innar har suka zo daidai kan damali kofar dakinsu inda suke yawan zama musamman idan ana kwalla rana saboda wajen akwai dan damshi damshi, tabarmar dake ajiye a wajen sabeeha ta warware ta shimfida kafin ta nufi uwar dakin su, labulen dakin ta daga tare da saka kai ciki, dakin bashida wani girma da alamu ciki da parlor ne don naga harda yan kujeru guda biyu sai ledar daki saidan fridge, daga gefe kuma wata yar yaloluwar katifa ce, ko’ina fess fess babu qazanta sai kamshin turaren tsinke dake tashi.
Direct inda dan mataccen fridge dinsu yake ta nufa ta bude kafin ta zaro pure water guda daya mai dan sanyi.
Shiga blue rubutun dake Ζasa domin karanta cikakken shafin πππ Kuduba Comment Section Akawai number na da WhatsApp dina π π π π π π π π π π π π l



Comments