Skip to main content

Featured

Innalillahi wa inna ilaihi raji'uñ rasuwar zee diamond 💎 ta gargiza kanny wood

 Jiya tana cikin waÉ—anda mutane ke addu’ar Allah Ya ba su lafiya.  Yau kuma, abin da ya rage wa iyalanta, abokan aikinta da masoyanta shi ne addu’ar Allah Ya gafarta mata.  Wannan shi ne labarin da ya karya zuciyar masu kallon shirin Labarina a safiyar yau Litinin. An samu labarin rasuwar jarumar Zee Diamond, wadda aka fi sani da rawar Talatuwa Babar Bintalo, bayan ta shafe watanni tana fama da rashin lafiya. Rahotanni sun ce jarumar ta rasu ne da asubahin yau Litinin. Zee Diamond ta kasance daga cikin jaruman da masu kallon Labarina suka saba gani kuma suka sani ta hanyar rawar da take takawa, musamman matsayin Talatuwa Babar Bintalo. Rasuwarta ta zama babban rashi ga iyalanta, abokanta, abokan aikinta da kuma masoyan da suka saba ganin ta a cikin shirin. Wannan rasuwa ta sake tunatar da mutane yadda yanayin rayuwa kan sauya cikin lokaci.  Wanda mutane ke yi wa addu’ar samun lafiya a wani lokaci, cikin Ć™anĆ™anin lokaci sai a koma yi masa addu’ar samun rahama. A wanna...

Iran tabawa duniya mamaki yau kalli cikakkun wakilan data tura pakistan

 ..

Yayin da wakilan Amurka da Iran suka isa birnin Islamabad domin tattaunawar kawo


ƙarshen yaƙin Iran da Amurka, hankula sun koma kan su wane ne wakilan ɓangarorin biyu?


A irin wannan tattaunawa dai kowace ƙasa kan aika da ƙwararrun mutane ta fuskar diplomasiyya domin kare muradunsu.

Iran dai ta gabatar da sharuɗaɗɗa 10 da take son a amince da su domin kawo ƙarshen yaƙin, yayin da Amurka ta gabatar da 15.

Suwa ne wakilan ɓangarorin biyu?

  • Tawagar Amurka

JD Vance: Washinton ta aike da wakilai Ć™arĆ™ashin jagorancin mataimakin shugaban Ć™asar.


Ana sa ran Vance zai taka muhimmiyar rawa a tattaunawar.

A baya Mista Vance ya sha bayyana adawarsa da yaƙe-yaƙe, ya kuma nuna rashin goyon bayan ƙazancewar yaƙin Iran.

Steve Witkoff: Sakataren harkokin wajen Ć™asar, Steve Witkoff, wanda amini ne ga Shugaba Trump kuma Ć™wararren jami'in diplomasiyya.

Ya taka muhimmiyar rawa a manyan al'amuran duniya ciki har da batun tsagaita wuta a yaƙin Gaza da na Ukraine.

Jered Kushner: Suruki ne ga shugaba Trump, shi ma ya Ć™ware a fannin diplomasiyya.

Ya taka rawar gani a diplomasiyyar yankin Gabas ta Tsakiya, ciki har da yarjejeniyar Abraham Accord.

Kusher na gudanar da harkokinsa tsakanin kasuwanci da siyasar duniya.

  • Tawagar Iran

Wakilan Iran na ƙarƙashin jagorancin ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, wanda ƙwararren jami'in diplomasiiya ne.

Yana da gogewar kusan shekara 40 a fannin diplomasiyya, wanda ya sha shiga manyan tattaunawa musamman da Amurka kan shirin nukiliyar Iran.

Mohammad Bagher Ghalibaf : Kakakin majalisar dokokin Iran, wanda ya jagorancin rundunonin Ć™asar da dama a matsayin kwamanda a baya.

Ya taɓa riƙe muƙamin magajin garin birnin Tehran.

Ghalibaf ya kasance kan gaba a shafukan sada zumunta wajen mayar wa Amurka martani.

Waɗannan mutanen biyar za su yi amfani da gogewarsu ta aikin soji da siyasar duniya da kasuwanci da diplomasiyya wajen kawo ƙarshen yaƙin da aka shafe kusan kwana 40 ana gwabzawa.

Sakamakon tattaunawar da za a yi a Pakistan shi ne zai tantance makomar alaƙar Amurka da Iran.

Comments

Popular Posts