Skip to main content

Featured

Innalillahi wa inna ilaihi raji'uñ rasuwar zee diamond 💎 ta gargiza kanny wood

 Jiya tana cikin waɗanda mutane ke addu’ar Allah Ya ba su lafiya.  Yau kuma, abin da ya rage wa iyalanta, abokan aikinta da masoyanta shi ne addu’ar Allah Ya gafarta mata.  Wannan shi ne labarin da ya karya zuciyar masu kallon shirin Labarina a safiyar yau Litinin. An samu labarin rasuwar jarumar Zee Diamond, wadda aka fi sani da rawar Talatuwa Babar Bintalo, bayan ta shafe watanni tana fama da rashin lafiya. Rahotanni sun ce jarumar ta rasu ne da asubahin yau Litinin. Zee Diamond ta kasance daga cikin jaruman da masu kallon Labarina suka saba gani kuma suka sani ta hanyar rawar da take takawa, musamman matsayin Talatuwa Babar Bintalo. Rasuwarta ta zama babban rashi ga iyalanta, abokanta, abokan aikinta da kuma masoyan da suka saba ganin ta a cikin shirin. Wannan rasuwa ta sake tunatar da mutane yadda yanayin rayuwa kan sauya cikin lokaci.  Wanda mutane ke yi wa addu’ar samun lafiya a wani lokaci, cikin ƙanƙanin lokaci sai a koma yi masa addu’ar samun rahama. A wanna...

Yanzu yanzunan Iran ta qaddamar da sabbin hare hare wa izraila

 Getty Images

Rundunar sojin Isra'la ta ce sabbin hare-haren Iran sun nufi cikin Isra'ila.

Cikin wani saƙo da rundunar ta wallafa a shafinta na Telegram, ta ce tana ƙoƙarin kakkaɓo hare-haren yayin da aka aike da saƙon gargaɗi ta waya ga mazauna yankunan da hare-haren suka dosa.


Kafar yaɗa labaran IRIB, mallakin gwamnatin Iran ta ce an fara ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami na Iran.

A wani labarin na daban ma'aikatar tsaron UAE ta ce ta kakkaɓo makamai masu linzami huɗu da jirage marasa matuƙa 25 da Iran ta harba ƙasar a ranar Lahadi.

Cikin wani saƙo da ma'aikatar ta wallafa a shafinta na X, ta ce tun bayan fara yaƙin Iran ta kakkaɓo makaman linzami fiye da 350 da jirage masara 

Comments

Popular Posts