Wani aikin sai kasar Iran
Operation Epic Fury
Dabarun yaƙi sun canza salo tun ranar da aka ruguza Baghdad a cikin kwanaki 11 na shekarar 2003.
Iran ta kalli gawar Saddam Hussain, daga nan ta zana wani darasi guda me girma domin tasan cewa itama wannan shirin nasu Yana zuwa gareta, darasin kuwa shine, kada ka taɓa zama da KAI guda ɗaya, domin duk lokacin da takobin makiyi ya sareshi zai zama baka da wani zabin cigaba da numfashi.
A yau, da duniya take murnar nasarar Operation Epic Fury, fadar White House tana cikin fargabar wani abu da aka binne shi meter 500 a ƙarƙashin sahara.
Wannan abinda nake fadamuku yanzu ba labari ba ne ko tatsuniya; tsari ne na kariya da aka gina shi ya zama Autonomous, ma'ana na'urar da take gudanar da kanta ba tare da mai sarrafata ba. Tun a shekarar 2005, IRGC Janar Jafari ya ƙaddamar da abin da ake kira Mosaic Doctrine.
Dabarar ita ce; Fasa rundunar soji gida 31, sannan soja daya daga kowane lardi. Kowane lardi na Iran yana da nasa duniyar; nasa makaman, nasa sadarwar, da nasa umarnin yaƙi da aka riga aka sanya wa hannu (Pre-authorized).
Idan kiran waya ya daina fita daga Tehran, to wannan Shiru (Silence) shi ne babban umarnin fara harba makami. Ko an kashe shugaba, ko an ruguza helkwatar tsaro, wannan na'urar ba ta da Off-Switch. Machine ne da aka gina shi don ya tsira ko da mahaliccinsa baya nan. Shi ya sa ko da an kai hari kan manyan jami'ai, Axis of Resistance yana ci gaba da kai hare-hare kamar babu abin da ya faru.
Akwai wani sirri a ƙarƙashin ƙasa, Missile Cities. Bom ɗin Amurka mafi nauyi, GBU-57 Massive Ordnance Penetrator (MOP) mai fam 30,000, yana iya fasa kankare harna tsawon meter 200 ne kacal. Amma Iran ta gina biranen makamanta meter 500 a ƙarƙashin duwatsu. Matukan jirgin Amurka wato pilots dinsu sun san wannan zazzafar gaskiyar, cewa za ka iya shafa fentin ƙofar shiga, amma ba ka isa taɓa abin da yake ciki ba, wato zaka iya yin duk abinda zakayi na sauke bam da harsashi a kofar shiga amma kome zakayi bazaka samu asalin gurin da makaman Nan suke ba.
Waɗannan ramin ba wurin ɓoyewa mutane ba ne; sansanonin harba makamai ne, rumbun man fetur, da wuraren kwana da aka kera su don su jure kowane irin farmaki na tsawon shekaru.
Duniya tana mamakin yadda ƙasa ɗaya take jure takunkumi, barazanar ruguza gwamnati, da yaƙe-yaƙe na tsawon shekaru 45. Shugabannin Amurka shida (tun daga Reagan, Clinton, Bush Junior, Obama, Trump, zuwa Biden) duka sun zo sun wuce, amma tsarin Iran yana nan daram ƙarƙashin jagora ɗaya, Khamenei, tun 1989. Wannan ba zallar sa'a ba ce; Resilience (juriya) ne aka gina ta a matsayin makami.
Sun gano cewa miƙa wuya da tattalin arziki ba zaɓi ba ne me kyau.
Lokaci a Iran yana bin nasa tafarkin ne na musamman, inda aka gina na'urar yaƙi da take aiki ko da operator dinta ya riga ya tafi.
Gaskiyar magana ita ce, A duniyar 2026, idan baka fahimci cewa yaƙi ya koma Systems (tsari) ba, to za ka ci gaba da yaudarar kanka da hotunan nasarar ƙarya. Nasarar gaske ba ita ce ruguza gine-gine ba; ita ce iya tsayar da na'urar da ba ta da maballin kasheta. Kuma har yanzu, babu wani injiniyan yaƙi a Yamma da ya gano inda maballin Mosaic Doctrine yake, domin maballin yana cikin wannan Shirun.
Idan baka zama Analyst ba, to lalle zaka zama abincin propaganda.
#fblifestyletyle @topfans



Comments