Shekh sani Khalifa yarasu
Idan rahotannin rasuwar Sheikh Sani Khalifa gaskiya ne, to gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ce za ta ɗauki cikakken alhakin hakan.
An kama shi yana cikin ƙoshin lafiya, amma aka hana shi beli har kusan watanni 3 yanzu. An kuma hana lauyoyinsa da iyalansa samun damar ganinsa, wanda hakan ya saba wa umarnin Federal High Court, duk da cewa yana fama da rashin lafiya.
Ya zama wajibi gwamnati ta fito ta bayyana gaskiya!
Amma yadda gwamnatin tarayya a ƙarƙashin jagorancin Tinubu ke karya kundin tsarin mulki ba tare da tsoro ba, abin matuƙar tayar da hankali ne.
Inji Lauya Abba Hikima



Comments