Skip to main content

Featured

Innalillahi wa inna ilaihi raji'uñ rasuwar zee diamond 💎 ta gargiza kanny wood

 Jiya tana cikin waɗanda mutane ke addu’ar Allah Ya ba su lafiya.  Yau kuma, abin da ya rage wa iyalanta, abokan aikinta da masoyanta shi ne addu’ar Allah Ya gafarta mata.  Wannan shi ne labarin da ya karya zuciyar masu kallon shirin Labarina a safiyar yau Litinin. An samu labarin rasuwar jarumar Zee Diamond, wadda aka fi sani da rawar Talatuwa Babar Bintalo, bayan ta shafe watanni tana fama da rashin lafiya. Rahotanni sun ce jarumar ta rasu ne da asubahin yau Litinin. Zee Diamond ta kasance daga cikin jaruman da masu kallon Labarina suka saba gani kuma suka sani ta hanyar rawar da take takawa, musamman matsayin Talatuwa Babar Bintalo. Rasuwarta ta zama babban rashi ga iyalanta, abokanta, abokan aikinta da kuma masoyan da suka saba ganin ta a cikin shirin. Wannan rasuwa ta sake tunatar da mutane yadda yanayin rayuwa kan sauya cikin lokaci.  Wanda mutane ke yi wa addu’ar samun lafiya a wani lokaci, cikin ƙanƙanin lokaci sai a koma yi masa addu’ar samun rahama. A wanna...

Matar da tahaifi Yaya biyar akank ta rasu

 Innalillahi wa inna ilaihir raji’un….


Ai tunda naga Abis Fulani ya bada labarin matar nan wai da kanta ta haifi yata biyar nasan akwai matsala…


Yaushe ma aka haifi daya,masu biyun basu share ba…bare har biyar?


Basuyi scanning bane?

Basu da kudin yin CS ne?

Ko kuwa yaya akayi?



Kafin ku fara koya min tauhidi nasan Allah daya ne,kuma nasan kowa idan lokacin sa yayi zai mutu…

Amma ya kamata mutum ya mutu bayan anyi iya kokari abu ya gagara


Makusantan matar nan basuyi kokari ba tunda suka barta har tayi nakudar yara biyar ba tare da sunyi shirin kaita an cire su ba…


Sai a Nigeria…amma ko nakudar ma bai kamata a barta tayi ba bare har ta haihu da kanta

Comments

Popular Posts