Skip to main content

Featured

Innalillahi wa inna ilaihi raji'uñ rasuwar zee diamond 💎 ta gargiza kanny wood

 Jiya tana cikin waɗanda mutane ke addu’ar Allah Ya ba su lafiya.  Yau kuma, abin da ya rage wa iyalanta, abokan aikinta da masoyanta shi ne addu’ar Allah Ya gafarta mata.  Wannan shi ne labarin da ya karya zuciyar masu kallon shirin Labarina a safiyar yau Litinin. An samu labarin rasuwar jarumar Zee Diamond, wadda aka fi sani da rawar Talatuwa Babar Bintalo, bayan ta shafe watanni tana fama da rashin lafiya. Rahotanni sun ce jarumar ta rasu ne da asubahin yau Litinin. Zee Diamond ta kasance daga cikin jaruman da masu kallon Labarina suka saba gani kuma suka sani ta hanyar rawar da take takawa, musamman matsayin Talatuwa Babar Bintalo. Rasuwarta ta zama babban rashi ga iyalanta, abokanta, abokan aikinta da kuma masoyan da suka saba ganin ta a cikin shirin. Wannan rasuwa ta sake tunatar da mutane yadda yanayin rayuwa kan sauya cikin lokaci.  Wanda mutane ke yi wa addu’ar samun lafiya a wani lokaci, cikin ƙanƙanin lokaci sai a koma yi masa addu’ar samun rahama. A wanna...

Maitamakin gwamnan kano ya ajiye mukaminsa

 Ƙungiyar Kwankwasiyya ta sanar da cewa Mataimakin Gwamnan Jihar Kano ya miƙa murabus daga mukaminsa.



Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da mai magana da yawun ƙungiyar, Dakta Habibu Sale Mohammed ya fitar.


Sanarwar ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin tabbatar da zaman lafiya da kuma bai wa ofishin damar gudanar da aikinsa yadda ya kamata ba tare da tangarda ba.


Sanarwar ta ce murabus ɗin ba yana nufin amincewa da zarge-zargen da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi ba, inda Mataimakin Gwamnan ya jaddada cewa yana da tsabtataccen tarihi a aikin gwamnati.


Sanarwar ta ƙara da cewa ya ɗauki matakin ne domin kauce wa rikice-rikicen siyasa da ka iya kawo tsaiko ga tafiyar gwamnati da ci gaban jihar.


Haka kuma sanarwar ta bayyana cewa zai mai da hankali wajen ƙarfafa ƙungiyar Kwankwasiyya da tsara dabarun siyasa gabanin zaɓen 2027.


Ƙungiyar ta buƙaci magoya bayanta da al’ummar jihar da su kasance masu bin doka tare da ci gaba da goyon bayan shugabanci nagari.

Comments

Popular Posts