Skip to main content

Featured

Innalillahi wa inna ilaihi raji'uñ rasuwar zee diamond 💎 ta gargiza kanny wood

 Jiya tana cikin waɗanda mutane ke addu’ar Allah Ya ba su lafiya.  Yau kuma, abin da ya rage wa iyalanta, abokan aikinta da masoyanta shi ne addu’ar Allah Ya gafarta mata.  Wannan shi ne labarin da ya karya zuciyar masu kallon shirin Labarina a safiyar yau Litinin. An samu labarin rasuwar jarumar Zee Diamond, wadda aka fi sani da rawar Talatuwa Babar Bintalo, bayan ta shafe watanni tana fama da rashin lafiya. Rahotanni sun ce jarumar ta rasu ne da asubahin yau Litinin. Zee Diamond ta kasance daga cikin jaruman da masu kallon Labarina suka saba gani kuma suka sani ta hanyar rawar da take takawa, musamman matsayin Talatuwa Babar Bintalo. Rasuwarta ta zama babban rashi ga iyalanta, abokanta, abokan aikinta da kuma masoyan da suka saba ganin ta a cikin shirin. Wannan rasuwa ta sake tunatar da mutane yadda yanayin rayuwa kan sauya cikin lokaci.  Wanda mutane ke yi wa addu’ar samun lafiya a wani lokaci, cikin ƙanƙanin lokaci sai a koma yi masa addu’ar samun rahama. A wanna...

Iran na daf da rushe yahudawa akawo agaji

 Wallahi lran ta razana su na gaske 



Yau lran ta hari wani sansanin Amurka na soji dake kan tekun india wadda makamin yayi yafiyar kilomita dubu hudu kamar daga lagos na Nijeriya zuwa Nairobi na kenya .


A sanadiyar haka duniya ta dau mamaki na gaske kowa na fadin albarkacin bakinsa .


A daren nan wani babba daga Ixraila ya fara jefa barazana ga kaashen turai cewa wannan makamain fa lran ba dan lxraila ta kera ba face don turai .


Bari ku gani 


Iran ta harba makami mai linzami mai matakai biyu (intercontinental ballistic missile) wanda ke da nisan kai har kilomita 4,000, inda aka nufa da shi wani sansanin Amurka a tsibirin Diego Garcia.


Ya ƙara da cewa waɗannan makamai ba don kai hari kan Isra’ila aka tsara su ba, amma suna da ikon kai hari zuwa manyan biranen Turai. A cewarsa, birane kamar Berlin, Paris, da Rome na cikin yankin da za su iya kai wa hari kai tsaye(Clash report)


Tabbas kuma anan yayi gaskiya saboda wannan makami mai dogon zango ya fi karfin harin yar karamar kasa kamar lxraila.

Comments

Popular Posts